Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sojin Sudan ya ce tattaunawa da 'yan adawa tana gudana sannu a hankali
2019-05-27 10:05:45        cri

Kwamitin soji dake mulkin kasar Sudan (TMC), ta sanar a jiya Lahadi cewa, tattaunawar dake gudana tsakaninsa da manyan kungiyoyin adawar kasar tana gudana sannu a hankali.

"Tattaunawar tana gudana sannu a hankali. Idan lamarin ya dore a haka, ana sa ran lamarin zai yi sanadiyyar samun ci gaba wanda zai dace da muradun al'ummar kasar Sudan da kuma tabbatar da tsaron kasar Sudan." kakakin TMC Shams-Eddin Kabashi shi ne ya bayyana hakan.

Ya jaddada aniyar TMC ta tabbatar da mika mulki cikin lumana ga fararen hula, yana mai cewa, kwamitin sojin kasar mai mulki yana wakiltar dakarun sojojin kasar da sauran jami'an tsaron kasar, kuma ita ce babbar mai jagorantar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Tattaunawar tsakanin TMC da kungiyoyin adawa na Freedom da Change Alliance tana fuskantar turjiya sakamkon rashin daidaito kan batun rabon iko a majalisar kasa da kuma tsarin wakilci.

TMC da kungiyoyin adawa a baya bayan nan sun amince da raba madafun iko a bisa tsarin shugabanci, wanda ya kunshi gurabe a majalisar ministoci da majalisar dokokin kasar.

Bangarorin biyu sun amince cewa, wa'adin da za'a dauka na mika mulki zai kai shekaru 3, inda za'a yi amfani da watanni shidan farko wajen tabbatar da samun zaman lafiya a duk fadin kasar ta Sudan.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China