Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani jami'i na Sin ya yi bayani game da ziyarar shugaba Xi Jinping a Koriya ta Arewa
2019-06-22 16:20:21        cri
Tun daga ranar 20 zuwa 21 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ke ziyara a kasar Koriya ta Arewa bisa gayyatar da aka yi masa. Bayan gama ziyarar, darektan hukuma mai kula da harkokin cudanya ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin Song Tao ya yi bayani game da ziyarar shugaba Xi Jinping ta wannan karo.

Song Tao ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping ya kai ziyarar a lokacin da ake cika shekaru 70 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Koriya ta Arewa, kana wannan ne karo na farko da shugaba Xi Jinping ya kai ziyara kasar tun bayan da ya zama shugaban kasar Sin, don haka ziyarar na da babbar ma'ana wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Hakazalika, an ce shugaban ya kai ziyarar a lokaci mai muhimmanci ga shawarwarin shimfida zaman lafiya a zirin Koriya. A cewar jami'in hakan zai sa kaimi ga warware batun zirin Koriya ta hanyar siyasa da tabbatar da zaman lafiya a zirin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China