Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya dawo birnin Beijing bayan ziyarar aiki a Koriya ta arewa
2019-06-21 19:14:31        cri
Babban sakataren kwamitin koli na JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya dawo nan birnin Beijing da yammacin Juma'ar nan, bayan kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Koriya ta arewa.

Shugaba Xi ya samu rakiyar mai dakinsa Peng Liyuan, da mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kuma mamba a sakatariyar kwamitin na koli, kana babban darakta a ofishin kwamitin koli na JKS Ding Xuexiang, da Yang Jiechi, shi kuma mamba, kana direktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS. Sauran sun hada da memban majalissar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar ta Sin Wang Yi. Sai kuma mataimakin shugaban kwamitin kasa na majalissar bada shawara kan harkokin siyasa, kuma shugaban hukumar tsara samar da ci gaba da gudanar da gyare gyare ta kasar Sin He Lifeng. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China