![]() |
|
2019-06-21 09:30:22 cri |
Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bikin liyafar maraba da zuwa, wanda takwaransa Kim Jong-un na Koriya ta arewa ya shirya masa jiya Alhamis a Pyongyang, fadar mulkin kasar.
A daren wannan rana, Xi Jinping da mai dakinsa Madam Peng Liyuan, bisa rakiyar takwaransa Kim Jong-un da uwar gidansa Madam Ri Sol Ju, sun kalli raye-raye da wake-wake a filin wasa na "May Day" dake Pyongyang, tare da jama'ar kasar. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China