![]() |
|
2019-05-09 09:52:44 cri |
Da yake jawabi a lokacin kaddamar da rahoton daidaita kasuwar hada-hadar kudade a Nairobi, Luke Ombara, daraktan tsare-tsare a hukumar kula hada-hadar kudi ta Kenya (CMA), ya ce tsarin ciniki dake amfani da fasahar zamani (ATS) a duk fadin shiyyar yana fuskantar hasarori wanda hakan na iya shafar harkokin kasuwancin shiyyar.
Ombara ya ce, an taba fuskantar irin wannan kalubake a watan Oktoban shekarar 2018, lamarin da ya haddasa samun jinkiri a lokacin gudanarwar cinikayya har na tsawon sa'o'i sama da 4, wanda hakan ya haifar da samun koma baya na ribar da aka samu a harkokin cinikayya a wannan rana.
Ombara ya ce, ingantaccen tsarin zai kara samar da damammaki wajen bunkasa kasuwar hada-hadar kudade da bunkasuwar kayayyakin more rayuwa a nan gaba a tsakanin shiyyar har ma da duniya baki daya.
"Amfani da tsarin fasahar zamani mai karfi a kasuwannin samar da kayayyakin more rayuwa zai samar da tsaro, da rangwame, da kuma inganci a tsarin kasuwanni wanda hakan zai yi matukar bunkasa harkokin cinikayya," in ji shi. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China