Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin MDD sun yi gargadi game da saurin karuwar yunwa a gabashi da kahon Afrika
2019-06-05 11:00:24        cri
Hukumomin MDD 2 sun yi gargadi game da hadarin yunwa da tamowa dake saurin karuwa a gabashi da kahon Afrika, musammam Somalia, idan aka samu karancin ruwan sama ko kuma aka rasa baki daya.

Kakakin ofishin hukumar samar da abinci ta MDD a Geneva, Herve Verhoosel, ya bayyanawa taron MDD cewa, hukumar ta damu matuka da yuwuwar saurin karuwar yunwa da tamowa a yankin gabashi da kahon Afrika, idan ba a samu ruwan sama sosai ba.

Ya ce la'akari da yanayin rani tun Oktoban bara da karancin ruwan sama tsakanin watan Afrilu da Mayu, hukumar WFP ta yi kiyasin mutanen dake fama da yunwa, wadanda kuma ke bukatar tallafin abinci a kasasheb Habasha da Somalia da Kenya da Uganda da Djibouti, ka iya kai wa tsakanin miliyan 14 da 17 a cikin watan Augusta.

Haka zalika yayin taron, kakakin hukumar UNCHR mai kula da 'yan gudun hijira ta majalisar, Babar Baloch, ya bayyana gabanin ranar muhalli ta duniya da ake yi a yau Laraba cewa, hukumar ta yi kira da a gaggauta kara taimakawa mutanen da fari ya raba da matsugunansu a Somalia. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China