Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sabunta layin dogon kasar Sin da ta shafe shekaru 100
2019-06-12 12:28:55        cri

A yayin da aka shimfida karfe na karshe na layin dogo a ranar Laraba na hanyar jirgin karkashin kasa a jami'ar Tsinghua dake Beijing, an gina dukkan tsawon hanyar jirgin kasan mai saurin tafiya tsakanin Beijing zuwa Zhangjiakou.

Titin jirgin kasan na asali da ya hada biranen biyu, wacce aka fi sani da hanyar jirgin kasa ta farko mai zaman kanta wadda kasar Sin ta tsara kuma ta gina, ta fara aiki ne a shekarar 1909.

An tsara hanyar jirgin inda za'a iya tafiyar kilomita 350 a kan kowace sa'a guda, sabuwar hanyar jirgin mai nisan kilmita 174, za ta yi matukar takaita lokacin da ake dauka wajen yin tafiye-tafiye tsakanin babban birnin kasar Sin wanda ya hade makwabtan birane dake lardin Hebei zuwa tafiyar sa'a daya kacal, kuma zai yi matukar rage cinkoson ababen hawa a birnin, kana zai taka muhimmiyar rawa wajen karbar bakuncin gasar wasannin motsa jiki na duniya na lokacin hunturu na shekarar 2022 na Beijing.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China