Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta rubanya kokarin kawar da talauci ga masu bukata ta musamman
2019-06-12 11:03:45        cri

Gwamnatin kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen kawar da talauci, kuma a shirye take ta tallafawa mutanen dake da bukatar musamman, in ji jakadan kasar Sin.

Akwai mutane miliyan 85 Sinawa masu bukata ta musamman a fadin kasar Sin, adadin ya wuce duk wata kasa a duniya, in ji Ma Zhaoxu, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya bayyana hakan ne a gefen babban taron MDD na tsara dokokin kare hakkin mutane masu bukatar musamman karo na 12.

"Domin gina ingantacciyar al'umma, bai dace mu kyale wani mutum dake da lalurar nakasa a baya ba." in ji jakadan na kasar Sin.

Sakamakon irin wahalwalu na musamman da masu bukata ta musamman ke fama da su, gwamnati ta kara yawan kudaden da take warewa ga bangaren tallafawa marasa galihu, da yin kwaskwarima ga bangaren kula da lafiyarsu, da samar da damammakin gyare gyaren gidajen kwanansu, da nufin biyan muradunsu, in ji mista Ma.

Sakamakon yin aiki tukuru, adadin masu fama da lalurar nakasa ya ragu zuwa miliyan 1.7 a karshen shekarar 2018 daga adadin miliyan 6 a shekarar 2014, a cewar jakadan na Sin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China