Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bayyana matsaya game da takaddamar ciniki tsakaninta da Amurka a MDD
2019-05-18 16:21:04        cri

Ma Zhaoxu, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya jagoranci wani taro a helkwatar MDD dake birnin New York a ranar 17 ga wata game da dangantakar ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka. Jawabinsa ya gabatar da cikkaken bayani game da halin da ake ciki kan tattaunawar Sin da Amurka tun daga watan Maris din shekarar 2018, inda ya bayyana matsayin kasar Sin da kuma yin watsi da zarge zarge marasa tushe da ake mata.

Ma Zhaoxu ya ce, tawagar jami'an hukumomin cikini da tattalin arziki na bangarorin biyu sun sha gudanar da tattaunawa a lokuta daban daban. Kasar Sin ta sha nanata matsayinta na neman a warware dukkan wata takaddama ta hanyar tattaunawa, kuma a ko da yaushe kofarta a bude take na shiga tattaunawa, da tuntubar juna cikin gaskiya da zuciya daya, kuma tana iyakar kokarinta domin ganin an kare moriyar dukkannin bangarorin biyu. To sai dai kuma, duk da halin gaskiya da nuna kwazo da bangaren Sin ke nunawa, da kuma manufarta ta tabbatar da samun daidaito da cin moriyar juna, amma Amurka ba haka take yi ba, lamarin da ke kara ruruta wutar takaddamar cinikayya da dangantakar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, wannan nauyi ne gaba daya dake bisa wuyan bangaren Amurka. A game da batun takaddamar ciniki, kasar Sin ba ta son shiga yaki, amma kuma ba ta jin tsoron yakin. Kasar Sin ba ta fargabar duk wani matsin lamba daga ketare. Abin da muka kudiri aniya shi ne kare hakkokinmu da moriyarmu bisa matsayin doka.

Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Amurka zabi ne mai muhimmanci, amma kasar Sin ba za ta yi sakaci da muhimmiyar moriyarta ba. Kasar Sin ta yi Allah wadai da matsayin da Amurka ta dauka na buga harajin kwastam, wanda hakan bai dace da moriyar kasar Sin ba, da ita kanta Amurkar, har ma da duniya baki daya. Kara buga harajin kwastam ba zai warware matsaloli ba. Muna fatan Amurka da Sin za su yi aiki tare domin kare martabar juna da moriyar juna bisa tsarin girmama juna da cin moriyar juna da daidaito domin cin gajiyar dukkannin bangarorin biyu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China