Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya bukaci a warware matsalar Libya a siyasance
2019-05-22 11:02:40        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya yi kira da yi amfani da hanyoyin siyasa wajen warware batun Libya.

Ma Zhaoxu, ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD cewa, akwai bukatar rungumar mafita a siyasance, yana mai cewa, kasar Sin ta yi ammana cewa, dole ne a warware batun Libya a siyasance.

Ya kara da cewa, dole ne a tabbatar da tsaron fararen hula tare da inganta yanayin jin kai a kasar.

Ma Zhaoxu, ya bukaci kasashen duniya su kara hada hannu, sannan su martaba cikakken 'yancin da ikon kasar Libya.

Jakadan ya ce, ya kamata kasashen dake da tasiri su yi yunkurin warware sabanin dake tsakanin bangarori daban daban na kasar, da taimaka musu aminta da juna da samar musu ingantaccen tallafi domin cimma tsagaita bude wuta da komawa teburin sulhu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China