Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin mulkin soji da 'yan adawar Sudan sun lashi takobin cimma yarjejeniya
2019-05-21 14:28:22        cri

Yayin da suke ci gaba da tattaunawa, kwamitin mulkin soji na rikon kwarya, da kawance 'yan adawa na kasar Sudan, sun lashi takobin yin aiki tare don cimma yarjejeniya cikin gaggawa.

Wata sanarwa da bangarorin biyu suka fitar, ta ce har yanzu kwamitin da kawancen 'yan adawa, dake rajin samar da sauyi da 'yanci, na da sabanin ra'ayi kan wakilan soji da na fararen hula a cikin kwamitin mulkin na riko da kuma batun shugabancin sabuwar gwamnati.

Kwamitin sojin wanda ke da alhakin jan ragamar kasar, bayan hambarar da tsohon shugaba Omar al-Bashir, da kuma bangaren adawar, sun amince da wasu batutuwa da suka shafi ikon kwamitin da majalisar ministoci da ta dokoki. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China