Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Amurka ce ta haddasa duk wani koma baya game da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya
2019-06-04 20:45:35        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce duk wani kwan gaba kwan baya da ake samu, game da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasar Amurka, bangaren Amurkar ne ya haifar da shi, duba da yadda Amurkar ke keta matsayar da ake cimmawa, take kuma nuna halin rashin dattaku.

Geng Shuang ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai da aka gudanar a jiya Litinin, yana mai cewa, batun Amurka ta zargi Sin da laifin karya hurumin yarjejeniya, juyawa gaskiya baya ne da kuma yunkurin muzanta Sin.

Wasu rahotanni dai sun nuna cewa, ofishin wakilcin hada hadar cinikayya na Amurka, da ofishin baitulmalin kasar, sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa a ranar 3 ga wata, suna masu nuna rashin jin dadi game da takardar bayani da Sin ta fitar, wadda ta bayyana matsayin Sin din game da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu. Sanarwar ta ce Sin din ta yi nadama.

Game da hakan, Geng Shuang ya ce sanarwar ta Amurka na kunshe da juyawa ainihin gaskiya baya. Ya ce takardar bayani da Sin ta fitar ta fayyace cewa, duk wani koma baya da aka samu game da shawarwarin sassan biyu alhaki na wuyan Amurka, domin ita ce ke karya matsayar da aka cimma, take kuma nuna halin rashin dattaku. Ya ce zargin da Amurka ta yiwa Sin na keta matsayar da ake cimmawa ba gaskiya ba ne, hasali ma dai Amurka ce ke juyawa gaskiya baya, tare da yunkurin muzanta kasar Sin.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China