2019-06-10 12:53:05 cri |
Ministan kudi na kasar Sin Liu Kun ya halarci taron tare da yin jawabi, inda ya yi nuni da cewa, an kara samun rashin tabbaci a fannin raya tattalin arzikin duniya a halin yanzu, ana fuskantar ra'ayin bada kariya ga cinikayya a duniya. Ya kamata bangarori daban daban su sa lura kan hadarin koma bayan tattalin arziki, da tabbatar da tsarin bangarori daban daban bisa ka'idoji, da warware matsaloli cikin adalci yadda ya kamata. A halin yanzu, an samu rashin daidaito a kasashe da suka ci gaba, ya kamata wadannan kasashe su kara taka muhimmiyar rawa a wannan fanni. Daukar matakan bada kariya ga cinikayya a tsakanin bangarori biyu ba su taimakawa daidaita matsalar rashin daidaito kan tsarin bangarori daban daban ba, kana za su kawo illa ga samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Sin ta kiyaye samun bunkasuwar tattalin arziki a bana. Gwamnatin kasar Sin za ta dauki wasu matakan yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje don sa kaimi ga bude kofa da samun bunkasuwar tattalin arziki mai inganci, da kuma samun wadata a duniya baki daya. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China