Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da a dakatar da bude wuta a Tirabulus
2019-05-14 14:27:50        cri
Babban magatakarar MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a dakatar da bude wuta a Tirabulus fadar mulkin kasar Libiya bisa dalilai na jin kai.

Mr. Guterres ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakin kakakin sa Farhan Haq, yana mai cewa hakan zai bayar da damar fitar da marasa lafiya daga birnin, da ma sauyawa masu gudun hijira, da bakin haure matsugunai.

Jami'in ya ce MDD na ci gaba da damuwa, game da tasirin da tashe tashen hankula ke haifarwa a birnin da kewayen sa.

Sama da mutane 2,000 ne tashe tashen hankula na baya bayan nan suka jikkata, baya ga wasu daruruwa da suka rasu tun bayan barkewar tashin hankulan watan Afirilun da ya gabata, tsakanin gwamnatin dake samun goyon bayan MDD da sojoji masu helkwata a gabashin kasar, a yankunan Tirabulus da kewaye.

Ya ce yawan wadanda fadan na baya bayan nan ya shafa na karuwa, inda aka samar da karin bayanai game da halin da ake ciki a yanzu haka. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China