Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai kamata Amurka ta zargi Sin da kasancewa kasa mai bin tafarkin watsi da tsarin kwadago da na tattalin arziki ba
2019-06-03 20:24:52        cri

A ranar Asabar 1 ga watan nan ne ma'aikatar tsaron Amurka, ta gabatar da wani rahoto mai taken "manufar ma'aikatar tsaron Amurka kan harkokin tekun Indiya da Pasifik" a shafin ta na intanet, inda ta bayyana cewa, kasar Sin kasa ce mai bin tafarkin watsi da tsarin kwadago da na tattalin arziki, kuma za ta lalata tsarin harkokin duniya.

Game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya yi nuni da cewa, wannan zargi ne da ba shi da tushe ko kadan, ba zai kuma yiyu kasar Sin ta amince da shi ba. Jami'in ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce ta farko da ta sa hannu kan "ka'idojin MDD", kuma kawo yanzu, ta riga ta shiga kungiyoyin kasa da kasa sama da 100 da gwamnatocin kasashen duniya suka kafa, kana ta riga ta daddale yarjeniyoyin da aka kulla tsakanin bangarori daban daban fiye da 5000, haka kuma kasar Sin kasa ce wadda ta aika da mafi yawan sojojin kiyaye zaman lafiya a cikin kasashe biyar, wadanda ke da kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD.

Jami'in ya kara da cewa, duk da cewa Amurka ta kan bayyana manufar bin tsarin kasa da kasa, amma hakika tana nuna fin karfi ga sauran kasashe, ko ta aiwatar da manufar ba da kariya ga moriyar kanta, a don haka Sin na fatan wasu Amurkawa za su amince da hakikanin abubuwa na gaskiya, su daina zargi kasar Sin kamar yadda suke so, haka kuma su kara mai da hankali kan aikin shimfida zaman lafiya da samun ci gaba a duk fadin duniya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China