Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya zanta da 'yan jaridun muhimman kafofin watsa labarun Rasha
2019-06-05 11:23:41        cri
Gabanin ziyararsa ta aiki a tarayyar Rasha, da halartar taron dandalin tattauna hadin kan tattalin arzikin kasa da kasa karo na 23 da za a shirya a birnin St. Petersburg, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da manema labaru na wasu muhimman kafofin watsa labaru na kasar ta Rasha a jiya Talata, ciki har da kamfanin dillancin labaru na TASS, da jaridar Russian Gazeta.

Game da batun dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Rasha, Xi Jinping ya bayyana a yayin zantawar cewa, bayan ci gaban da aka samu na tsawon shekaru 70, dangantakar abota ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu tana samun bunkasuwa mai kyau da ba a taba ganin irinta ba a tarihi. Ya ce Kasashen biyu suna gudanar da hadin kai sosai a harkokin kasa da kasa, lamarin da ya kara kuzari kan yanayin duniya.

Xi ya kara da cewa, yanzu kasashen biyu na fuskantar sabuwar damar ci gaban dangantakar dake tsakaninsu, yana mai cewa, a yayin ziyararsa, yana fatan tsara shiri da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, kan makomar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba, da nufin ciyar da dangantakar zuwa wani sabon matsayi.

Game da makomar tattalin arzikin kasar Sin kuwa, Xi ya bayyana cewa, shekaru 70 bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, musamman ma shekaru 40 da fara kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, kasar Sin ta samu gagaruman nasarori a fannin ci gaban tattalin arziki, inda har ta kasance babbar kasa ta biyu a karfin tattalin arziki, kuma babbar kasa ta farko ta fuskokin kirkire-kirkire da cinikayyar kayayyaki da kuma kudin musanya da aka tanada.

Har ila yau, ya ce kasar Sin na da tabbacin yanayin samun dauwamamman ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata, kuma tana cike da imani da karfin gwiwar tinkarar kalubale daban daban.

Bayan haka kuma, Xi ya ba da amsoshi kan batutuwan da suka shafi halin Syria, Venezuela, da tsanantar gaba tsakanin Amurka da Iran a fannin siyasa da dai sauransu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China