Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#Takaddamar cinikin Sin da Amurka# Sin ta fitar da takardar gwamnati kan matsayin da ta dauka yayin tattaunawar ciniki tsakaninta da Amurka
2019-06-02 12:12:28        cri

Yau Lahadi gwamnatin kasar Sin ya fitar da wata takarda game da matsayin da ta dauka yayin da take gudanar da tattaunawar cinikayya da kasar Amurka, domin gabatar da cikakken bayani kan gudanarwar tattaunawar cinikayya dake tsakaninta da Amurka, tare kuma da bayyana matsayin da take dauka kan batun.

A cikin takardar gwamnatin, an yi nuni da cewa, tun daga watan Maris na shekarar 2018 kuwa, gwamnatin Amurka ta tayar da takaddamar cinikayya da kasar Sin, har kasar Sin ta ga tilas ta mayar da martani domin kiyaye babbar moriyar kasa da al'ummunta, a sa'i daya kuma, har kullum kasar Sin nace kan matsayinta na daidaita matsala ta hanyar yin hadin gwiwa, amma dole ne a gudanar da hadin gwiwa bisa tushen adalci, ba zai yiyu ba kasar Sin ta amince da matakin da zai lalata moriyar halal ta al'ummunta. Kasar Sin ba ta son yakin cinikayya, amma ba ta ji tsoron yakin ba ko kadan, matsayin da kasar Sin ta dauka kan batun ba zai canja ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China