Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya rubuta wasika don ba da amsa ga yaran yankin musamman na Macau
2019-06-01 15:50:56        cri
Gabanin ranar yara ta duniya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasika a jiya Juma'a, ga daliban dake makarantar firamaren dake karkashin makarantar sakandare ta Hou Kong, ta yankin musamman na Macau, don kara musu kwarin gwiwa, tare kuma da taya duk yaran kasar Sin baki daya murnar ranar yara ta duniya.

A cikin wasikar, Xi Jinping ya ce, zane-zanen da daliban makarantar suka yi sun yi kyau, yana mai yabawa kalamai da halayyarsu.

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya nuna cewa, daliban su ne furannin kasa, kuma makomar yankin Macau. Yana fatan daliban za su gaji kyakkyawar al'adar makarantarsu ta kaunar kasa da yankin Macau, kuma su yi kokarin karatu da girma cikin koshin lafiya, don taka rawa kan raya Macau da farfado da kasar Sin a nan gaba. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China