Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban hukumar wayar Sin: Dole kamfanin jigilar kaya na jarin waje ya bi dokar kasa
2019-06-02 15:13:00        cri

Yau Lahadi shugaban hukumar kula da aikin gidan waya ta kasar Sin Ma Junsheng ya yi bayani game da batun kamfanin FedEx mai jigilar kayayyaki cikin sauri na Amurka cewa bai yi jigilar kayayyaki bisa adireshin da aka rubuta ba a kasar Sin yayin da yake zantawa da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin ya ce, dole ne daukacin kamfanonin jigilar kayayyaki cikin sauri su bi dokokin kasar Sin, kada su lalata hakki da moriyar halal na kamfanoni da masu bukatar hidimar jigilar kayayyaki cikin sauri na kasar Sin.

Ma Junsheng ya jaddada cewa, an kai karar kamfanin na FedEx kotu domin yin bincike kan aikinsa, lamarin da zai kiyaye oda a kasuwar jigilar kayayyaki cikin sauri a kasar Sin, dole ne kuma ya kiyaye hakki da moriyar halal na kamfanoni da masu bukatar hidimar jigilar kayayyaki cikin sauri na kasar Sin, haka kuma zai amfani tsaron sadarwa da tattalin arzikin kasar Sin.

Ma Junsheng ya bayyana cewa, kasuwar jigilar kayayyaki cikin sauri ta kasar Sin ta yi girma matuka, yanzu haka tana samun bunkasuwa cikin sauri, kasar Sin tana maraba ga kasashen duniya da su zuba jari a kasuwar, amma dole ne su gudanar da aiki bisa tushen bin dokokin kasar Sin, kana dole ne su kiyaye hakki da moriyar halal na kamfanoni da masu bukatar hidimar jigilar kayayyaki cikin sauri na kasar Sin, bai dace ba su daina samar da hidima bisa dalilin da ba na kasuwanci ba, kana bai dace ba su lahanta hakki da moriyar halal na kamfanoni da masu bukatar hidimar jigilar kayayyaki cikin sauri na kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China