Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yayin da yarjejniyar AFCTA ta fara aiki, AU ta bukaci a kara inganta hulda tsakanin nahiyar da Kasar Sin ta fuskar ababen more rayuwa
2019-06-01 15:54:58        cri
Kwamishinan harkokin cinikayya da masana'antu na Tarayyar Afrika AU Albert Muchanga, ya yi kira da a kara zurfafa hulda tsakanin Sin da Afrika, domin bada gudunmuwa ga nasarar yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci na nahiyar(AFCTA), wadda ta fara aiki a ranar Alhamis.

Albert Muchanga, ya ce a kullum, nahiyar a shirye take ta kara karfafa hadin gwiwa da Kasar Sin, musammam wajen samar da ababen more rayuwa da za su hade nahiyar, wanda ke da matukar muhimmanci ga saukaka cinikayya karkashin yarjejeniyar ciniki mara shinge.

A cewar Jami'in, ana sa ran Sin da Afrika, wadanda yanzu haka ke hadin gwiwa a bangarori daban-daban, ciki har da raya kayayyakin ababen more rayuwa a fadin nahiyar, za su gaggauta ayyukansu da nufin cimma burin yarjejeniyar ta gudanar da ciniki mara shinge.

Ya kuma jaddada cewa, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya za ta bunkasa hadin gwiwa domin gaggauta burin Tarayyar Afrika na samar da ababen more rayuwa da za su hade nahiyar.

A ranar Alhamis ne jagoran tawagar Sin a AU, Liu Yuxi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yarjejeniyar ta ciniki cikin 'yanci, za ta taimaka wajen karfafa huldar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Afrika da kasar Sin.

Ya ce Kasar Sin na maraba da nasarorin gina yankin na ciniki cikin 'yanci, da mara baya ga inganta tsarin sadarwar sufuri a Afrika, kuma a shirye take ta yi aiki da nahiyar wajen inganta ciniki mara shinge. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China