Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dole ne tattaunawa tsakanin Sin da Amurka ta zamo bisa tushen martaba juna
2019-05-28 09:46:46        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce dole ne duk wata tattaunawar cinikayya da za ta gudana tsakanin Sin da Amurka, ta zamo bisa tushen martaba juna, da yanayi na daidai wa daida, da cin moriyar juna.

Lu Kang ya yi wannan tsokaci ne yayin wani taron manema labarai, biyowa bayan kalaman da shugaban Amurka Donald Trump ya yi a kasar Japan, inda aka rawaito shi yana cewa, a yanzu haka kasar sa ba ta da wani shiri na cimma yarjejeniya da Sin.

Mr. Lu ya ce, a dan tsakanin nan, tsagin Amurka ciki hadda wasu manyan jami'an kasar, sun rika furta wasu kalamai game da shawarwarin cinikayya da ake gudanarwa tsakanin Sin da Amurka. A wasu lokutan su kan ce za a cimma matsaya, yayin da a wasu lokutan kuma su ce za a fuskanci wasu kalubale kafin cimma matsayar.

To sai dai kuma a cewar sa, bangaren Sin na ci gaba da tsayawa kan matsayi guda, cewa duk wani sabani tsakanin kasashe biyu, kamar irin wanda ke gudana tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya, na bukatar warwarewa ta hanyar tattaunawa, da cimma daidaito cikin lumana.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China