Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya yi shawarwari tare da shugaban kasar Nijer
2019-05-29 11:38:40        cri


Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari tare da shugaban jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, wanda ke ziyara a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin a jiya Talata. Ya ce a halin yanzu, Sin da Nijar sun yi imani da juna a fannin siyasa, suna hadin gwiwa da juna a fannoni daban daban. Kaza lika Sin tana son yin kokari tare da Nijar wajen aiwatar da ayyukan da aka cimma daidaito, a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da kara yin hadin gwiwar dake tsakaninsu don amfanin jama'arsu.

A ranar 28 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bikin maraba da zuwan shugaban jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, a babban filin dake bakin kofar dakin taron jama'ar kasar Sin dake nan birnin Beijing. Shugaba Issoufou zai gudanar da ziyarar sa a nan kasar Sin tsakanin ranekun 26 zuwa 30 ga wannan wata, bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi masa.

A gun shawarwarin da suka yi a wannan rana, shugaba Xi Jinping ya yabawa shugaba Issoufou, bisa kokarin sa na sada zumunta a tsakanin Nijar da kasar Sin, da kuma tsakanin Afirka da Sin. Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin da Nijar 'yan uwa ne, kuma abokai na kusa. Xi ya yi jawabin cewa,

"Bayan da shugaba Issoufou ya kama aiki, an kara inganta imani da juna a tsakanin Sin da Nijar a fannin siyasa, da kuma hadin gwiwa da juna a fannoni daban daban. Dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta kasance misali na sada zumunta, da yin hadin gwiwa don samun moriyar juna a tsakanin Sin da Afirka. Kaza lika Sin tana fatan yin kokari tare da Nijar, wajen aiwatar da ayyukan da aka cimma daidaito a kan su, yayin taron koli na Beijing, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da fadada hadin gwiwarsu, da sada zumunta a tsakaninsu don amfanar jama'arsu baki daya."

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ya kamata Sin da Nijar su ci gaba da fahimtar juna, da imani da goyon baya ga juna, kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, da kuma musayar fasahohin sarrafa kasa, da gudanar da ayyukan gwamnatin kasar, da kuma samun ci gaba a kasar. Ya ce ya kamata kasashen biyu su kara yin hadin gwiwa bisa tsarin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka, da aiwatar da ayyukan hadin gwiwa a fannonin ayyukan more rayuwa, da zaman rayuwar jama'a, da makamashi, da aikin noma da sauransu. A cewar sa, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Nijar wajen yaki da ta'addanci, da tabbatar da zaman lafiya a yankin, da sa kaimi ga MDD, ta yadda za ta samar da goyon baya ga sojojin hadin gwiwa na kasashe 5 dake yankin Sahel.

Har ila yau Sin tana son samar da gudummawa ga jamhuriyar Nijar a fannin aikin ba da jinya da sauransu, da kara yin mu'amala da juna a fannonin al'adu, da matasa, da mata, da masana da sauransu, wanda hakan zai kara fahimtar juna a tsakanin jama'arsu.

A nasa bangare, shugaba Issoufou ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin ta samar da muhimmiyar gudummawa ga zamantakewar al'ummar dan Adam. Kana bunkasuwar tattalin arzikin Sin, ta kawar da talauci na jama'a da dama, da kuma sa kaimi ga cimma burin samun bunkasuwa na MDD na shekarar 2000. Ya ce,

"A madadin jama'ar jamhuriyar Nijar, ina taya Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin, da yabawa jama'ar Sin bisa nasarori da suka samu, da raya tsarin gurguzu na musamman na Sin a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin. Musamman a fannin tattalin arziki. Bayan da Sin ta fara yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje a shekaru 70 na karnin da ya gabata, sannu a hankali an samu bunkasuwar tattalin arziki, yanzu haka ta zama kasa ta biyu mafi ci gaban tattalin arziki a duniya."

Shugaba Issoufou ya ce, shawarar "ziri daya da hanya daya" wadda shugaba Xi Jinping ya gabatar ta shaida tunanin samun moriyar juna, wadda za ta amfani dukkan duniya. Kasashen Afirka sun yabawa Sin, da ta raya dangantakar dake tsakanin ta da nahiyar Afirka, bisa tunanin nuna gaskiya da sahihanci, da nuna godiya ga shugaba Xi, bisa gabatar da shirye-shirye 8 na raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, yana mai fatan kasashen Afirka za su kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin kiyaye zaman lafiya da raya kasa. Haka kuma, jamhuriyar Nijar ta nuna goyon baya ga manufar Sin daya tak, da kuma kokarin cimma nasarar kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, kasar tana son shiga aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya".(Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China