Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani harin 'yan bindiga ya yi sanadin mutuwar mutane 23 a Nijeriya
2019-05-29 09:15:50        cri

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta ce mutane 23 sun mutu sanadiyyar harin da wasu 'yan bindiga suka kai wasu kauyuka a jiya Talata.

Kakakin rundunar Mohammed Shehu, wanda ya tabbatar da harin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce kauyukan da abun ya shafa sun hada da Tunga da Kabaje dake yankin karamar hukumar Kaura-Namoda na jihar.

Ya ce, yanzu komai ya daidaita a yankunan, yana mai cewa, 'yan sanda da sojoji na aikin sintiri a yankin.

Wani jami'in karamar hukumar ya shaidawa Xinhua cewa, sama da 'yan bindiga 100 ne suka shiga kauyukan kan babura a lokacin da mazauna ke hanyarsu ta zuwa gona.

Har yanzu ba a san musababbin harin ba, domin kawo yanzu, babu wata kungiya a kasar da ta dauki alhakinsa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China