Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan Najeriya sun damke bata gari 56 a jihar Kaduna
2019-05-29 08:55:26        cri

Jami'an 'yan sandan Najeriya sun yi nasarar kama wasu bata gari kimanin 56, wadanda suka hada da masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga dake aikata ta'addanci a jihar Kaduna dake shiyyar arewacin kasar.

Ali Janga, babban jami'in 'yan sandan jihar, ya shedawa manema labarai rahoton cafke bata garin, a wani yunkuri na kakkabe ayyukan bata gari a fadin jihar, ya kara da cewa, jihar Kaduna ba za ta ci gaba da zama wata maboyar bata gari ba.

Ya ce 'yan sandan za su ci gaba da yin aiki tukuru bisa tsarin kwarewar aikin 'yan sanda na kasa da kasa.

A jihar Kaduna, dubban fasinjoji ne ke fuskantar barazanar hare haren 'yan bindiga a kan titunan mota.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China