![]() |
|
2019-05-24 09:10:46 cri |
Gwamnatin Nijeriya, ta tabbatar da tsare wani matashi mai shekaru 24, wanda ya kware wajen samar da kayayyaki ga kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Shugaban hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, Ibrahim Abdullahi, ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Aliyu Muhammed ne a ranar 25 ga watan Afrilu, biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu.
Jami'in ya ce, an kama Aliyu Muhammed ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta kai wasu kayayyaki ga kungiyar Boko Haram.
Ibrahim Abdullahi, ya shaidawa Xinhua cewa, wanda ake zargin da sauran abokan huldarsa sun ba da gudunmuwa daban-daban ga hare-haren da kungiyar ke kai wa kan gine-ginen gwamnati da cibiyoyin addinai da kasuwanni a cikin Maiduguri, babban birnin jihar, da kewayansa.
Aliyu Muhammad dake ikirarin matukin keke napep ne a cikin birnin Maiduguri, ya ce kungiyar Boko Haram ta horar da shi ne kimanin watanni 6 da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China