Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya zai rusa majalisar ministocinsa a 28 ga Mayu
2019-05-23 10:16:02        cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna alama a jiya Laraba cewa, zai rusa majalisar ministocinsa a ranar 28 ga watan Mayu, a yayin da ake shirin rantsar da sabuwar gwamnatin kasar a makon gobe.

A wani taron ban kwana da majalisar ministocin da aka gudanar a Abuja, wanda shugaba Buhari ya bayyana shi a matsayin na karshe, a wa'adin mulkinsa na farko, shugaban ya umarci ministocinsa da su ci gaba da zama a kan mukamansu har zuwa ranar Talata ta makon gobe.

Shugaban kasar ya bukaci dukkan ministocinsa da su mika ragamar aikinsu ga manyan sakatarorin ma'aikatunsu, kana su mika takardun barin aiki ga sakataren gwamnatin tarayya a wannan rana.

A ranar 29 ga watan Mayu, za'a rantsar da sabuwar majalisar ministocin kasar, a dandalin taro na Eagle Square dake babban birnin kasar Abuja. Sai dai za'a gudanar da wani dan karamin biki ne, kamar yadda ministan yada labaran kasar Lai Mohammed, ya fada, a farkon wannan makon.

Shugaba Buhari, ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Fabrairun wannan shekara, inda zai shafe wa'adin mulki a karo na biyu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China