Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya ba da umarnin binciken kisan manoma 18 a arewacin kasar
2019-05-23 09:29:40        cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa game da kisan manoma kimanin 18 da wasu 'yan bindiga suka yi a jihar Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin kasar, inda ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Da safiyar ranar Talata ne aka hallaka manoman a cikin gonakinsu dake kauyen Batsari a jihar Katsina.

A wata sanarwar da ofishin shugaban kasar ya fitar, shugaba Buhari ya bayyana lamarin da cewa rashin hankali ne inda ya umarci jami'an 'yan sandan kasar da manyan hafsoshin tsaro na kasar da su gaggauta kafa tawagar da za ta nazarci faruwar lamarin, tare da kai daukin gaggawa ga jihar, kana su mika masa rahoton sakamakon aikinsu.

Shugaban na Najeriya ya ba da umarni ga manyan hafsoshin tsaron kasar da su binciko yadda bata gari ke gudanar da ayyukansu, sannan su dauki dukkan matakan dakile ayyukan nasu a nan gaba.

Sanarwar ta tabbatar da cewa, an yiwa shugaba Buhari karin haske game da yadda ake shirya ayyukan bata gari da yadda 'yan siyasa ke daukar nauyin hare haren da ake kaddamarwa a jihar Katsina da sauran sassan arewacin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China