in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara shaida yadda kasar Sin ke kara bude kofa ga ketare a Hainan
2019-03-29 14:01:01 cri

A taron dandalin tattaunawar Asiya da aka shirya a bara a garin Boao na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping, ya sanar da wasu manyan matakai guda hudu, ciki har da kara fadada hanyoyin shigar da jarin waje a kasuwar Sin, da samar da yanayin zuba jari mai jawo hankali, da kara kiyaye 'yancin mallakar fasaha, da kuma sa himma wajen kara shigo da kayayyaki a kasar, matakan da suka soma kokarin bude kofar kasar ga waje na sabon zagaye. Bayan shekara guda, a yayin taron dandalin tattaunawar na Boao na bana, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya kara bayyana wasu alamun karfafa bude kofa ga kasashen ketare. A lardin Hainan wanda ya kasance muhimmiyar taga ta kasar Sin, wajen yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen ketare na tsawon shekaru 40, an kara shaida yadda kasar Sin ke kokarin kara bude kofarta ga kasashen waje.

Ba shakka bude kofa ga ketare, yana daya daga cikin muhimman dalilan da suka sa kasar Sin ta samu nasarori ta fuskar bunkasar kasa cikin shekaru 40 da suka wuce. Sakamakon bude kofarta ga kasashen waje, ya sa cikin gajeren lokaci kasar Sin ta zama kasa ta biyu a duniya ta fuskar ci gaban tattalin arziki, kana kasa ta farko a duniya a fannonin kera kayayyaki, yin cinikin kaya, da musayar kudaden da aka adana. Jama'ar Sin sun ji dadin samun irin wadannan nasarori, tare da kara sanin cewa, nan gaba wajibi ne kasar Sin ta kara bude kofa ga waje, a kokarin raya tattalin arzikinta yadda ya kamata. Duk da sauye-sauyen da duniya ke fuskanta, kasar Sin ba za ta canza wannan manufa ba, wadda ta tsai da aiwatar da ita bisa halin da take ciki.

A bara, shugaba Xi Jinping ya jaddada a Boao cewa, kamata ya yi a dauki matakai cikin hanzari ba tare da bata lokaci ba. A cikin shekara guda da ta gabata, hukumomin kudi masu jarin waje sun samu ci gaba sosai wajen shiga kasuwar kasar Sin. Sa'an nan kuma, kasar Sin ta fito da wasu matakan rage yawan haraji da wasu kudade da ake biya da kyautata yanayin yin kasuwanci, ta kuma rage yawan kudin kwastam daga kashi 9.8 cikin dari zuwa kashi 7.5 cikin dari. Dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa da aka zartas da ita a yayin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a bana, ta tabbatar da rashin nuna bambanci tsakanin kamfanonin gida da waje, nuna musu adalci, lamarin da zai kara bude kofa ga kowa, da kuma tabbatar da zuba jari ba tare da rufa-rufa ba.

Ban da haka kuma, kasar Sin ta samu ci gaba kwarai wajen kiyaye 'yancin mallakar fasaha. A rahoton da Bankin Duniya da ya fitar, ya nuna cewa, matsayin kasar Sin ta fuskar yanayin yin kasuwanci ya karu da 32 cikin shekara guda kawai.

A shekara guda da ta wuce, kasar Sin ta aiwatar da manufofin bude kofa ga waje daya bayan daya, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta cika alkawarinta. Yanzu kasar Sin tana kokarin bunkasa tattalin arzikinta yadda ya kamata. Tana cin gajiyar damar da juyin juya hali ta fuskar kimiyya da fasaha na sabon zagaye da kuma sauye-sauyen masana'antu suka kawo mata, yayin da take tinkarar barazanar ra'ayin ba da kariyar ciniki, da ra'ayin kashin kai da kuma tsanantar matsalar cinikin duniya. Duk da manyan sauye-sauyen da take fuskanta, kasar Sin za ta kara azama kan bunkasar tattalin arzikinta ta hanyar kara bude kofa ga waje. Kasar Sin ba za ta taba rufe kofarta ba, sai ma ta kara bude kofarta. Kasar Sin ta tabbatar da aniyarta ta bude kofarta ga waje domin tinkarar rashin tabbaci a duniya.

A bikin bude taron dandalin tattaunawar Asiya ta Boao na bana, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da jawabi, inda ya jaddada cewa, kasar Sin za ta gaggauta tsara dokoki, da ka'idojin da za su tallafawa dokar zuba jari ta baki, kuma hakan zai kara fadada hanyoyin shigowar jarin waje, tare kuma da kara bude kasuwar hada-hadar kudi ga baki.

Ana iya gano cewa, duk wadannan matakai suna shafar fannonin shiga kasuwar Sin, da muhallin zuba jari, da kiyaye 'yancin mallakar fasaha, da kuma hadin kan fasaha da dai sauransu, wadanda ke zama muhimman fannonin da kasar Sin za ta dora muhimmanci a kai, a yayin da take kara bude kofa ga kasashen ketare, kana muhimman batutuwa ne da ke jawo hankalin masu jarin waje dake neman ci gaba a nan kasar Sin.

Kasar Sin ta ba da amsa cikin lokaci, da daukar matakai, domin biyan bukatunta na kara bude kofa ga kasashen ketare, tare kuma da amfanawa kasa da kasa wajen cin moriyar ci gabanta, kana sun nuna cewa, kasar Sin na daukar nauyin dake wuyanta game da neman ci gaban duniya. (Tasallah Yuan)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China