Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Najeriya na shirin farfado da kanana da manyan tsarin kiwon lafiya
2019-05-23 09:49:36        cri
Ministan kiwon lafiya na tarayyar Najeriya, Isaac Adewole, ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, kasarsa za ta fara aiwatar da wani tsari da jihojin kasar za su yi rijista da asusun kula da kiwon lafiya.

Ministan ya shaidawa majalisar dattawan kasar hakan, yayin da yake karin haske kan matsalolin asibitocin koyarwa dake sassan kasar cewa, za a aiwatar da tsarin ne kafin lokacin da ake tsammani.

Ministan ya kuma bayyana cewa, an tsara asusun ne ta yadda kudi zai rika fitowa daga babban bankin kasar zuwa cibiyoyin kiwon lafiya ba tare da wata matsala. Ya zuwa yanzu, jihohin kasar 22 daga ciin 36 na kasar, sun shiga cikin wannan shiri, yayin da ake saran shigar karin jihohi.

Gwamnatin tarayyar kasar dai, na ba da kaso 1 cikin 100 ne, yayin da ragowar masu cin gajiyar shirin ke ba da sauran kason kudaden tafiyar da asusun kiwon lafiyar da 'yan kasar ke bukata.

Bisa ga yadda ma'aikatar lafiyar kasar ta tsara ka'ijojin gudanar da wannan asusun, zai taimaka wajen rage dogaro kan manyan cibiyoyin kiwon lafiya

An dai fara cin gajiyar asusun kiwon lafiya ne, bayan samun amincewar majalisar dokokin kasar a shekarar 2018.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China