Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta mayar da martani kan tsokacin tsohon shugaban kasar dangane da Boko Haram
2019-05-22 10:33:54        cri

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana tsokacin tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo, da ya alakanta kabilanci da addini da kungiyar Boko Haram, a matsayin mai tunzuri kuma kai ya kawo rarrabuwar kawuna, ta na mai cewa, irin wadannan kalamai bai dace su fito daga bakin dattijon kasa irinsa ba.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, ministan yada labarai da raya al'adu na kasar Lai Mohammed, ya ce abun takaici ne yadda mutumin da ya yi gwagwarmaya don tabbatar da kasancewar Nijeriya matsayin tsintsiya madaurinki daya, shi ne wanda ke neman amfani da matsalolin kasar wajen raba kanta a lokacin da shekarunsa suka ja.

Ya ce, kungiyoyin Boko Haram da ISWAP dukkansu na ta'addanci ne, yana mai cewa, ba sa la'akari da kabila ko addini a lokacin da suke kai hare-harensu na rashin imani.

Ya ce, tun da aka fara rikicin Boko Haram, wanda ya faru karkashin idanun Obasanjo, ya kuma barke a shekarar 2009, kungiyar ta kashe musulmai fiye da mabiya sauran addinai, haka kuma ta kai hare-hare kan masallatai fiye da duk wani wurin ibada, kuma an sani cewa, ba ta barin wani saboda kabilarsa.

A don haka, ministan ya ce kalaman na Obasanjo abun dariya ne kuma mara ma'ana, kamar yadda suke na ban haushi da ka iya raba kan kasa mai mabiya addinai da kabilu daban daban kamar Nijeriya.

Ministan ya yi kira ga tsohon shugaban da kada ya bari adawarsa ta dakushe kaunar da yake yi wa kasar, yana mai cewa, ba wani abu ba ne idan ya janye furucin nasa tare da neman afuwar al'ummar kasar. ( Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China