Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ba za ta shirya wani gagarumin bikin rantsar da shugaban kasar ba
2019-05-21 09:40:15        cri

Ministan watsa labarai na Najeriya, Lai Mohammed, ya bayyana cewa, ba za a shirya wani kasaitaccen bikin rantsar da shugaban kasar a ranar 29 ga watan Mayu ba, sabo da tsimin kudi.

Ministan wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce, dan karamin bikin da za a shirya don fara wa'adi na biyu na mulkin shugaba Muhammadu Buhari, ya zama wajibi, "saboda kasar ba za ta iya shirya manyan bukukuwa biyu a cikin makonni biyu ba". A maimakon bikin da aka saba shiryawa na rantsar da shugaban kasar a ranar 29 ga watan Mayu, yanzu gwamnatin tarayyar Najeriyar ta gayyaci shugabannin kasashen duniya, don su halarci bikin ranar demokordiya ta farko da kasar za ta shirya a ranar 12 ga watan Yuni.

Kakakin gwamnatin Najeriyar ya ce, bukukuwan da tun farko aka shirya gudanarwar a bikin rantsar da shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, an mayar da su ranar 12 ga watan Yuni. Yana mai cewa, za a fara bikin sabuwar ranar demokiradiyar kasar a hukumance a wannan shekara, kamar yadda shugaba Buhari ya ayyana a shekarar 2018 da ta gabata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China