Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takaddamar ciniki a tsakanin Sin da Amurka ba ta kawo babbar illa ga tattalin arzikin Sin ba
2019-05-22 14:10:09        cri

A 'yan kwanakin baya, Amurka ta kara sanyawa kayayyakin kasar Sin dake cikin kasar harajin kwastam, da yunkurin tilastawa kasar Sin amincewa da bukatunta a yayin shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin jami'an kasashen na Sin da Amurka. Masanan Sin da dama sun bayyana cewa, takaddamar ciniki a tsakanin bangarorin biyu ba ta kawo babbar illa ga tattalin arzikin kasar Sin ba, kuma Sin tana da imani da karfin tinkarar matsalar.

Tun shekarar bara ne, Amurka ta fara kara sanyawa kayayyakin kasar Sin dake shiga kasar ta Amurka harajin kwasta, matakin da ya kawo illa ga wasu kamfanonin kasar Sin. Wani kamfanin samar da batir iri na Lithium na lardin Hubei na kasar Sin yana daya daga cikinsu. Mataimakin shugaban kamfanin Liu Qi ya bayyana cewa, kasar Amurka muhimmiyar kasuwar ketare ce ga kamfaninsa, yana kuma fitar da kaso 60 cikin 100 na kayayyakinsa zuwa kasar Amurka. A shekarar bara, a sakamakon karin harajin da Amurka ta sanyawa kayayyakin kasar Sin, kamfanin ya rage fitar da kayayyakinsa da dama zuwa kasar Amurka. Ko da yake kamfanin ya fuskanci matsala, amma Liu Qi ya ce kamfanin na da dabarar tinkarar wannan matsala. Ya ce,  

"Matakin farko da muka dauka shi ne inganta karfinmu na yin takara, da amfani da kudi wajen nazari da kyautata fasahohinmu. Muna son samar da wasu sabbin kayayyaki ta yadda za a mu kara karfinmu a kasuwa. A wannan karo, kasar Amurka ta sake sakawa kayayyakin kasar Sin harajin kwastam, wannan matakin ba zai yi mana wata illa ba. Daga watan Afrilu zuwa watan Satumba, tawagar manajojin kamfaninmu za su ziyarci masu sayayya na Amurka da suka dakatar da sayen kayayyakinmu, ta yadda za su sake dawowa sayen kayanmu. Yanzu muna da imani da karfi wajen tinkarar tasirin da sanya karin harajin zai yi mana a nan gaba."

Bisa sauye-sauyen da ake fuskanta a yanzu, karin kamfanonin samar da kayayyaki na kasar Sin sun gano cewa, idan ana son samun ci gaba, akwai bukatar su kara zage damtse da inganta karfinsu na kimiyya da fasaha da nazari, ta yadda za su inganta karfinsu na yin takara da tinkarar matsaloli da kuma samun ci gaba mai inganci. Alkaluman kididdigar tattalin arziki na nuna cewa, kamfanonin samar da kayayyaki masu fasahohin zamani na Sin suna samun saurin ci gaba. Tun daga watan Janairu zuwa watan Afrilu na bana, yawan jarin da aka zuba a fannin fasahohin zamani ya karu sosai. Yawan jarin da aka zuba a fannin samar da kayayyaki masu fasahohin zamani ya karu da 11.4 cikin dari, kana yawan jarin da aka zuba a fannin samar da hidima masu fasahohin zamani ya karu da kashi 15.5 cikin dari.

Mataimakin zaunannen shugaban kwalejin nazarin tsara manufofi da yanayin tattalin arziki na kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Wang Changlin yana ganin cewa, matsalar ciniki a tsakanin Sin da Amurka ba ta kawo babbar illa ga tattalin arzikin kasar Sin ba, domin Sin tana da kyakkyawar makoma da karfi wajen samun ci gaba. Ya ce,

"Takaddamar ciniki a tsakanin Sin da Amurka ta yi tasiri a gare mu, amma ba wata babbar illa ba ce. A hakika, muna iya daukar wasu matakai, bisa babbar kasuwar da muke da ita, da kyakkyawar makomar ci gaban kasarmu, da ma fifikonmu a fannonin tsarin mulki, da yawan tattalin arziki, da manyan bukatun cikin gida, wajen kawar da tasirin da kasashen waje suka haifar mana."

Sin tana da kasuwa mai yawan mutane kimanin biliyan 1 da miliyan 400, da cikakken tsarin samar da kayayyaki da karfin yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha a duniya. Musamman matakan kashe kudi na kasar Sin ya riga ya samar da gudummawa da ta kai kashi 70 cikin dari wajen bunkasa tattalin arzikin kasar. Game da wannan batu, shugaban gudanarwa na kwalejin kula da hada-hadar kudi na Jami'ar Renmin ta kasar Sin Wang Wen ya bayyana cewa,  

"Kasashen duniya suna begen samun kasuwar kasar Sin mai yawan mutane kimanin biliyan 1 da miliyan 400. Alkaluman kididdigar shekarar 2018 na nuna cewa, yawan kudin da aka kashe a kasuwar kasar Sin ya zarce na kasar Amurka, Sin ta kasance kasuwa mafi girma a duniya. Don haka, bisa wannan halin da ake ciki, Sin tana da karfin tinkarar matsalar karin harajin kwastam da aka sanyawa kayayyakinta." (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China