Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya bada jawabi a bikin bude taron tattaunawar wayewar kan Asiya
2019-05-15 13:32:30        cri

An bude taron tattaunawar wayewar kan Asiya a yau Laraba 15 ga wata a nan birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi.

Wannan taro dai ya samu halartar shugabannin kasashen Cambodia, Girka, Singapore, Sri Lanka, Armenia da sauransu da kuma shugaban kasar Mongolia da wakilan kungiyar UNESCO da dai sauran kungiyoyin kasa da kasa.

Taro mai taken "Tuntubar wayewar kan Asiya da koyi da juna da al'umma mai kyakkyawar makoma" ya jawo hankalin matasa, masana, ma'aikatan gwamnatoci da mambobin kungiyoyi daban-daban na kasashen Asiya 47 da na kasashe na sauran nahiyoyi. Ban da bikin budewar kuma, ana shirya wasu taruka da dama, da suka hada da gagarumin bikin nune-nunen al'adun Aiysa, makon wayewar kan Asiya, da dai sauran ayyukan masu ruwa da tsaki har 110. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China