![]() |
|
2019-05-13 14:14:24 cri |
Mista Xi ya ce, ya kamata mu sa kaimi ga mutunta al'adu daban-daban da raya al'adu mai jituwa, ta yadda za a maida al'adu daban-daban su zama wata gada da ta zurfafa zumuncin al'ummomi daban-daban, da sa kaimi ga bunkasuwar bil Adam, da mahadar da ta kiyaye zaman lafiyar duniya. Sin ne ta yi kiran a kira irin wannan taro, don kara tuntuba tsakanin matasa da kungiyoyin fararen hula da yankuna daban-daban da kafofin yada labarai na kasa da kasa, ta yadda za a kafa wani dandali na hadin kai tsakanin masana na fannoni daban-daban, don jama'ar Asiya suna iya more rayuwarsu ta tunani da kara himma da kwazo ga hadin kai tsakanin yankuna daban-daban. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China