Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya tattauna tare da sarkin kasar Saudiyya
2019-05-08 21:15:03        cri
A yau Laraba Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna tare da sarkin kasar Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud ta wayar tarho, inda ya yi nuni da cewa, Sin na dora muhimmanci sosai a kan raya huldar abokantaka a tsakaninta da Saudiyya, kuma tana daukar Saudiyya a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa wajen raya "ziri daya da hanya daya".

A nasa bangaren, sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud ya ce, yana taya kasar Sin murnar gudanar taron kolin dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan ziri daya da hanya daya, wanda a ganinsa zai taka muhimmiyar rawa, wajen raya ci gaban kasa da kasa da ma hadin gwiwarsu.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China