in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin laiman kwadi yana iya raga barazanar gamuwa da matsalar MCI dake shafar kwakwalwa
2019-11-28 15:46:48 cri

Masu nazari daga jami'ar kasar Singapore sun kaddamar da rahoton nazarinsu a kwanan baya cewa, idan tsoffafi sun ci laiman kwadi da ya kai giram fiye da dari 3 a ko wane mako, barazanar da suke fuskanta wajen gamuwa da matsalar MCI dake shafar kwakwalwa za ta ragu.

Matsalar MCI wata irin matsala ce dake shafar kwakwalwar tsoffafi, inda take shafar yanayin koyo da adana muhimman abubuwa, amma muninta ba ta kai ta cutar mantuwa ba. Masu nazarin suna ganin cewa, cin laiman kwadi yana iya taimakawa wajen rage barazanar gamuwa da matsalar MCI sakamakon kasancewar wani sinadari na musamman dake cikin laiman kwadi. 'Yan Adam ba sa iya sarrafa irin wannan sinadari a cikin jikinsu, sai ta cikin abincin da suka ci, laiman kwadi yana daya daga cikin muhimman abinci masu kunshe irin wannan sinadari

Daga shekarar 2011 zuwa 2017 ne masu nazarin na Singapore suka tattara bayanan da suka shafi tsayin jikin tsoffafi Sinawa masu shekaru fiye da 60 a duniya fiye da 600 da ke zaune a Singapore, da bugun jininsu, da yadda suke cin abinci a yau da kullum, da dai sauransu. Daga bisani kuma, sun kimanta kwakwalwar wadannan tsoffafi.

Masu nazarin ba su yi la'akari da tsawon shekarun wadannan tsoffafi, jinsinsu, al'adarsu ta shan taba ko giya, bugun jininsu da ko suna fama da ciwon sukari ko a'a ba. Sun gano cewa, gwargwadon tsoffi wadanda ba safai su kan ci dafaffun laiman kwadi ba, tsoffin da su kan ci dafaffun laiman kwadi da ya kai giram dari 1 da 50 a ko wane lokaci kuma sau biyu a ko wane mako, barazanar da suke fuskanta wajen gamuwa da matsalar kwakwalwa ko MCI ta ragu da rabi baki daya. Laiman kwadi ya aka yi nazari kansu a wannan karo, sun hada da wasu nau'o'i 6 da a kan ci da kuma kayayyakin da aka sarrafa daga gare su.

Kafin wannan kuma, masu nazarin sun gano cewa, yawan sinadarin da ake samu a cikin laiman kwadin da ke jinin masu fama da matsalar kwakwalwa ta MCI bai kai na takwarorinsu masu koshin lafiya ba. Nan gaba, masu nazarin za su ci gaba da gudanar da nazarinsu don kwatanta wannan sinadari da sauran sinadarai da ke cikin tsirrai, kamar sinadaran da ke cikin ganyayen shayi, don tabbatar da amfaninsa wajen sassauta matsalar MCI. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China