in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hulda tsakanin Sin da Afirka
2015-12-04 08:25:52 cri
Assalamu alaikum, zuwa gas ashen hausa na CRI, kamar yadda Tasllah Yuan, ta aiko min da sako daga ranar daya zuwa biyar ga watan Disamba domin hulda da ke tsakanin Sin da Afrika.

A hakikanin gaskiya hulda tsakanin Sin da Afrika hulda ce data kunshi abubuwa da dama tun kafin samun 'yan cin kai daga turawan mulkin mallaka na kasashe da ban da ban da sukayi wa kasashen nahiyar afrika mulkin mallaka, hulda tsakanin kasar Sin da Afrika ta samo asali ne tun lokacin da ake cinikayya da nuna kimiya da fasaha ta wajen kere - kere da nuna irin al'adun Sin da Afrika inda ake nuna al'adun irin da ban da ban saboda da haka hulda tsakanin Sin da Afrika wata alakace ta kud da kud tsakanin kasar Sin da Afrika inda ake nuna gwaninta ko bajinta tsakanin Sin da Afrika.

Hulda tsakanin Sin da Afrika ba abin cewa sai dai alla san barka domin kuwa Sin ta taka rawar gani musamman a wannan lokaci inda ta bayyana manufofinta da kuma dangantaka tsakaninta da Afrika inda ta kera kayayyaki masu saukin kudi da mallaka da saukin mallaka ko kuma rikewa ga al'ummar nahiyar afrika manya da kanana, kayan da Sin ta kira sun samu karbuwa a nahiyar Afrika baki daya ciki da waje, saboda Sin ta samu shiga lungu da sako a nahiyar afrika don samun ba don komai ba, sai irin fasaha da kere-kere da kasar keyi musamman ga kasashe masu karamin karfi musamman ma a Afrika. Kanya da Kasar Sin ke kerawa sun hada da Wayar Salula, Talabijin, Firijin, Kofofin gida, Kwano na bugawa a gida, da dai sauran abubuwan more rayuwa wadanda ake amfani dasu birni da kauye a nahiyar afrika baki daya.

Hulda tsakanin Sin da Afrika wani cigaba ne da aka samu a tsakanin nahiyoyin biyu wajen musanya dalibai daga Afrika zuwa Sin, ko kuma daga Sin zuwa Afrika domin karatu da kuma koyon sana'a musamman 'yan Nijeriya na zuwa Sin domin karatu da koyo aiki na zamani wato fannin sana'o'in da Sin ki koyarwa, haka ma Sin ta turo wato musanyar dalibai zuwa afrika domin koyon harsunan kasashen afrika domin yin hulda da su a cikin sauki dan gane da kasuwanci da dai sauransu.

Hulda tsakanin Sin da Afrika wani bangare ko dangantaka domin kara dankon zumunci tsakanin Sin da Afrika wadda ta haka hulda ke kara kawo ci gaba domin idan muka dubi yadda zamani ya canja ko ketafiya kasar Sin ta samu daukaka a Afrika dama duniya baki daya wajen hulda da kasashen ketare domin samun shiga a lungu-lungu da sako sako na Africa, daga karshe muna fata hulda tsakanin Sin da Afrika zata kasance abin koyi ga sauran kasashe na duniya domin samun daukaka kamar yadda kasar Sin ta samu a wannan zamani.

GABA DAI GABA DAI KASAR SIN

GABA DAI GABA DAI AFRIKA

ALLAH YA DAUKAKA AMIN.

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v Hulda tsakanin Sin da Afirka 2015-12-04 08:25:52
v Cudanyar dake tsakanin Afrika Da Sin 2015-12-04 08:21:31
v Hulda tsakanin SIN da Africa 2015-12-02 20:59:38
v Dangantakar Kasar Sin da Afrika 2015-12-02 20:56:16
v Sako daga malam Anas Saminu Ja'en a jihar Kano ta Nijeriya 2015-12-01 15:59:45
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China