in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan cin kayan lambu da 'ya'yan itace na iya rage barazanar kamuwa da cututtukan da suka shafi huhu
2015-11-17 15:23:02 cri

Sanin kowa ne cewa, cin kayan lambu da 'ya'yan itace na iya kara wa mutum sanadarin bitamin C da sauran abubuwa gina jiki da dan-adam ke bukata matuka. Sakamakon sabon nazari da aka gabatar a kasar Birtaniya a kwanan baya ya nuna cewa, yawan cin kayan lambu da 'ya'yan itace na iya taimakawa wajen rage illar da gurbatacciyar iska ke haddasawa wa mutane, musamman ma yana da muhimmanci ga wadanda suke fama da cututtukan da suka shafi huhu su samu isasshen sanadarin bitamin C.

Masu nazari daga kwalejin jami'ar koyon kimiyya da fasaha ta smasarautar Ingila sun yi bincike kan mutane fiye da dari 2 da suke fama da ciwon asma ko kuma wani nau'in ciwon huhu na COPD, sun gano cewa, yayin da ake fama da gurbatacciyar iska mai tsanani, masu fama da ciwon wadanda ba safai su kan ci kayan lambu da 'ya'yan itace, kuma ba su da isasshen sinadarin bitamin C ba, nan da nan ciwon ke tashi, sasnnan su gamu da matsalar yin numfashi.

Masu nazarin na ganin cewa, hakan ya nuna cewa, Sinadarin Bitamin C na daya daga cikin sinadaran Antioxidants da ake yawan samu. Sinadaran Antioxidants suna iya kare dan Adam daga kamuwa da cututtukan dake addabar mutum sannu a hankali har ya tsufa da sauri. Watakila sakamakon shakar gurbatacciyar iska zai sanya mutane su kamu da ciwon zuciya, ciwon sankara ko kansa da cututtukan da suka shafi huhu.

Ban da haka kuma, masu nazarin sun gano cewa, yawancin mutanen da shekarunsu ya kai 54 amma bai zarce 74 a duniya dake shan taba sigari, to sune su ka fi fama da cututtukan da suka shafi huhu, kuma. Abun da ya kamata a lura da shi shi ne, wasu matasan da shekarunsu ya kai 18 kawai a duniya sun kamu da irin wadannan cututtuka ne sakamakon shakar gurbatacciyar iska.

Masu nazarin sun yi gargadi da cewa, yin kyakkyawan amfanin da sinadaran Antioxidants ba shi da nasaba da ko an sha taba ko a'a, ba shi da nasaba da ko an kamu da ciwon ko a'a, kuma ba shi da nasaba da shekarun mutane a duniya. Sinadarin Bitamin C ya fi taka rawa wajen kare masu shan taba da tsoffi masu fama da ciwon, don haka an ba da shawarar cewa, kamata ya yi a yawan ta cin danyen kayan lambu da 'ya'yan itace a kullum. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China