Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, jiya 13 ga watan Fabrairu ta kasance ranar rediyo ta duniya kuma saboda muhimmancin wannan rana ne na ga ya dace na dan yi wani sharhi dangane da irin gudunmawar da rediyo ke bayarwa wajen wayar da kai, ilimantarwa da kuma fadakarwa.
Abu ma fi muhimmanci dangane da rediyo shi ne sadar da zumunci tsakanin al'umma daban daban, ga misali tun kafin a kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Nijeriya a shekarar 1971, rediyo ta kasance wata hanyar sada zumunci da musayar ra'ayi tsakanin al'ummomin kasashen Sin da Nijeriya, wato tun bayan da sashen Hausa ya fara watsa shirye-shiryensa zuwa nahiyar Afirka a shekarar 1963. Tun daga wannan lokaci ne kuma kawo yanzu sashen Hausa na Huasa ya ke kan aikin wayar da kan masu sauraro tare da fadakarwa dangane da tarihi, al'adu da kuma wayewar kan Sinawa na shekaru fiye da 5000.
Hakika, rediyo ta taka muhimmiyar rawa wajen ilimantar da ni sh'anin zaman rayuwar duniya tare da fahimtar al'adu daban daban daga nahiyoyin duniya. A duk lokacin da wani batu ya shigewa mai sauraro duhu, to zarar ya aika tambaya zuwa gidan rediyo sai ka ga an ba shi cikakkiyyar amsa cikin shirin nan mai farin jini na Amsoshin Wasikun ku. Saboda haka, rediyo tamkar wata makaranta ce wacce ke bayar da haske kan wasu al'amura na rayuwar mu ta yau da kullum. Saboda haka, mallakar rediyo ga dan Adam wata kyakkyawar dama ce ta samun ilimi da bayanai masu muhimmanci ba tare da zuwa makaranta ba.
Kazalika, rediyo kan taimaka wajen wayar da kan al'umma dangane da sha'anin kiwon lafiya, ga misali shirin, Kiwon lafiya da malama Tasalla Yuan ke gabatarwa yana taimakawa matuka wajen kula lafiyar jiki tare da daukan matakan kariya daga wasu cutukan. Ga kuma uwa-uba labarai da rediyo ke bayarwa cikin sauri fiye da sauran hanyoyin sadarwa kamar talbijin ko yanar gizo wato internet. Dalilin da ya sa kenan rediyo ke da farin jini ba wai kawai tsakanin mutanen birni ba har ma da na kauye. Wannan shi ne dalilin da ya sa har yanzu sha'awa ta da sauraron rediyo ke karuwa.
Ba zan taba mantawa da sashen Hausa na CRI ba, domin cikin shekaru kimanin 25 da na yi ina sauraron kafafen rediyo daban daban, CRI ce kan gaba wajen jan hankali na sakamakon shirye-shirye masu dadin ji da kuma yin goma ta arziki ga masu sauraronsa.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria