A gaskiya shirin masamman kan abuncin halal na kasar Sin ya kara wayin kai ga dubban masu sauraro a dangane da yanayin rayuwar musulmi a kasar Sin kana faya-fayen bidiyon da ake nuna wa masu sauraro wanda malama Fatima Inuwa Jibril take jagoranta a yankunan musulmi a kasar Sin ya zama wani saban salon yawan bude idanu da yawan shakatawa ta hanyar kallon faya-fayen bidiyo ga mu masu sauraro cikin sauki. Buba shakka, sashin Hausa na Radio kasar Sin kun cancanci babban yabo da girmamawa bisa kokarinsu na wayar da kan al'ummomin kasa da kasa a dangane da yanayin rayuwar musulmi da al'adunsu a kasar Sin da yawan shakatawa a kasar Sin da kuma sanar da mu masu sauraro hakikanin abubuwan dake faruwa a kasar Sin da Afirka da ma duk duniya baki daya.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.