in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar tawagar likitocin Sin a asibitin Kambodia--Wang Jinhua
2015-03-24 15:49:13 cri

Saboda yanayin gudanar da harkokin asibiti da fasahar likitanci a Kambodia ba su iya biyan bukatun aikin, kuma babu isasshen kayayyakin kiwon lafiya da na'urorin tiyata na zamani a asibitin, baya ga rashin bincike na yau da kullum yadda ya kamata. A cikin shekara daya da ta yi tana aiki a kasar, malama Wang da ma'aikatan tawagar likitocinta, sun ba da horo ga likitocin kasar ta hanyoyi iri daban daban, kamar yin tiyata cikin hadin gwiwa da dai sauransu, ta yadda suka koyar da fasahohin zamani cikin sauri.

Don gane da haka, Tony, wani likitan dan kasar Kambodia a asibitin na Preah Ket Mealea, ya ce, kwarewar shugabar nas Wang Jinhua kan aikinta, ta kasance abin koyi ga duk wanda ke aikin likitanci. Ya kuma kara da cewa, cikin shekara daya da ta yi tana aiki a kasar, malama Wang da ma'aikatan tawagar likitocinta sun ba da jinya ga jama'ar kasar da yawansu ya kai kusan dubu goma, kuma marasa lafiya da suka kamu da cututtuka masu yaduwa, ko sauran cututtuka sama da dubu daya sun warke bayan jinyar da suka yi musu. Ban da haka, sun samu nasarar aikin tiyata masu wuya guda dari biyu a asibitin. Alal misali sankarar kwakwalwa, ko cire kansa, da karayar kashi da ke sassan jiki da sauransu.

Jama'ar Kambodia kan dauki ma'aikatan tawagar ba da jinya a matsayin kwararru a matakin koli mafiya fifiko a aikin likitanci. Bugu da kari, ma'aikatar tsaron Kambodia ta baiwa malama Wang Jinhua "lambar yabon shimfida zaman lafiya" da "lambar yabon sada zumunta da zaman lafiya tsakanin kasashen Sin da Kambodia". (Maryam)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China