in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar tawagar likitocin Sin a asibitin Kambodia--Wang Jinhua
2015-03-24 15:49:13 cri

Asibitin babban birnin kasar Kambodia "Phnom Penh", shi ne asibiti na matsayin koli cikin manyan asibitocin sojin kasar, wanda kuma ke ba da jinya ga sojoji, da jami'an rundunonin sojin kasar, da kuma al'ummomin kasar. Ko da yake asibitin yana da fasahohi, da kayayyakin zamani da dama bisa taimakon da kasar Sin ke ba shi, a hannu guda ya gamu da matsaloli da dama yayin da tawagar likitocin Sin ke gudanar da aikinta a kasar.

Na farko shi ne, babu manufofin ba da jinya, da kiwon lafiya, da kuma gudanarwa cikin asibitin, don haka malama Wang ta fara koyar ma'aikatan asibitin daga tushe, kuma an samu sakamako cikin sauri sabo da kwarewarta a wannan aiki.

Kaza lika, babu ayyukan kashe kwayoyin cuta da kuma fidda ababen da ka iya yada cuta daga abubuwan da ake amfani da su a asibitin, inda bisa fasaharta kan aikin, malama Wang ta shirya aikin kashe kwayoyin cuta daga kayayyaki da wuraren aikin tiyata, wanda ya ba da tabbaci ga aikin kammala tiyata na farko cikin yanayi mai kyau.

Haka kuma, bisa kokarin da likitocin na Sin suka yi, yanayi da kuma fasahohin aikin kiwon lafiyar asibitin Preah Ket Mealea sun samu kyautatuwa matuka, tawagar ta kuma kafa tsarin ganin likitocin kwararru, domin kara tallafa wa marasa lafiya yadda ya kamata. Kaza lika, Wang Jinhua ta kuma kafa wani tsari na "sa hannun mutane uku a aikin tiyata", watau, kafin a fara tiyata, babban likita mai tiyata na kasar Kambodia, da babban likita mai ba da jagoranci na kasar Sin, da kuma shugaban tawagar kwararrun likitocin Sin, su uku kan sanya hannu kan takardar tiyata, domin tabbatar da alhakin likitan Kambodia, ta yadda za a iya ci gaba da kyautata manufofin asibitin yadda ya kamata.

Wani masanin tawagar kwararrun likitocin da kasar Sin ta tura zuwa kasar Kambodia rukuni na 10 Huang Zhigang, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, tasirin da malama Wang ta haifar game da manufofin asibitin na ba da muhimmin taimako cikin ayyukansu na yau da kullum ya yi matukar alfanu.

Bugu da kari, baya ga gudanar da aikinta yadda ya kamata, malama Wang ta kuma taimaka wa sauran ma'aikata, da ofisoshin asibitin wajen kyautata ayyukan da manufofin asibitin. Huang Zhigang ya kuma bayyana cewa, an kafa manufofin gudanarwa na asibitin masu yawa bisa taimakon malama Wang, irin manufofin da babu su kafin zuwan ta.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China