in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rayuwar likita Zhang Yueming a Kasar Guyana
2015-03-23 14:55:53 cri

Yayin da yake kula da aikinsa, Zhang Yueming ya gano cewa, ko da yake asibitin Georgetown na fama da matsalar rashin kayayyaki masu inganci, amma ya kasance wani asibiti mai kunshe da likitoci na kasashe daban daban, musamman ma wadanda suka zo daga nahiyoyin Asiya, da Afirka, gami da Amurka ta Arewa. Don haka akwai damar musayar ra'ayi tsakaninsu a fannin tunanin aikin likitanci. Hakan ya kasance wani muhalli mai kyau, amma ya kasance hade da yanayi maras kyau, wato jama'ar kasar Guyana ba su san yadda za su kula da lafiyar matan da suka haifu, ko ma kula da jarirai sosai ba, idan an kwatanta da yadda ake kula da su a kasar Sin. Wannan al'adar ta sa masu aikin jinya na kasar Guyana rashin maida cikakken hankali kan farfadowar jikin macen da ta haifu, gami da lafiyar jikin jajirai.

Don daidaita wannan matsala, Zhang Yueming ya kan yi bincike kan wasu alkaluman da aka samu wadanda ke bayyana lafiyar jikin majiyyata a ko wace rana. Bisa jagorancinsa, sannu a hankali, tunanin likitocin Sinawa na maida hankali kan lafiyar jikin mahaifiya, da yara, ya fara shiga cikin zukatan likitocin kasar Guyana. Zhang Yueming ya ce, "Ba wai haifuwar yaro kadai ne aiki ba, a'a, dole a maida hankali kan ko an fid da jini sosai? Ko jariri yana da lafiya? Don haka na kan yi binciken wasu alkaluma, inda na ga akwai matsala, zan tambayi mai kula da majiyyata, tilas ne a samu wani dalilin da ya haddasa matsalar."

Bayan da Zhang Yueming ya yi watanni 4 yana aiki a kasar Guyana, jama'ar kasar, da hukumomin kasar sun amince da shi sosai, ganin yadda yake da kwarewar aiki, haka zalika yana kokari kwarai da gaske. Saboda haka, a watan Oktoba na shekarar 2012, an daga matsayin Zhang Yueming zuwa darektan sashin mata da haihuwa na asibitin Georgetown, kuma jami'i mai kula da aikin da ya shafi mata da haihuwa na ma'aikatar lafiyar kasar Guyana. Bisa sabon matsayinsa ne, Zhang Yueming ya samar da gudunmowa sosai a kokarin kyautata tsarin aikin sashin na mata da haihuwa na asibitin Georgetown, gami da tsara wasu nagartattun manufofin kiwon lafiya a kasar Guyana.(Bello Wang)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China