in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rayuwar likita Zhang Yueming a Kasar Guyana
2015-03-23 14:55:53 cri

A watan Maris na shekarar 2015, mista Zhang Yueming, kwararren likita kuma mataimakin darektan sashin kula da mata da haihuwa, na asibitin farko na jami'ar Suzhou ta kasar Sin, ya samu wani sakon e-mail da aka aika masa daga kasar Guyana dake latin Amurka, sakon da ya kasance wasikar gaisuwa da wata majiyyaciyar da ya taba kula da ita ta aiko masa. Duk da cewa ya koma kasar Sin watanni 6 da suka wuce, amma sakon irin wannan ya kan sanya shi tunawa da zamansa a Guyana, inda ya ba da taimakon jinya.

Ya zuwa yanzu kasar Guyana ta kasance wuri mafi nisa da Zhang ya taba zuwa. A watan Yuni na shekarar 2012, an zabi likitoci 15 daga asibitoci 5 na biranen Suzhou da Changshu, dukkansu a lardin Jiangsu, don kafa tawagar likitoci ta 10 da kasar Sin ta tura zuwa kasar Guyana, inda Zhang Yueming ya kasance daya daga cikin likitocin.

Zhang Yueming ya ce, "An sanar da bukatar kafa wata tawagar likitoci a farkon shekarar 2011. Daga baya aka zabi wasu kwararrun likitoci, domin halartar jarrabawa, kafin a tabbatar da sunayen wadanda za a tura. A cikin tawagarmu, akwai mutane 8 da suke da matsayin ilimi na dokta, ko kuma wadanda ke karatu domin samun digiri na dokta. Malamina Yang Weiwen ya taba gudanar da aikin tallafi a Zanzibar, don haka ya lallashe ni don na halarci aikin tallafi a ketare. Hakan ya zama daya daga cikin dalilan da suka sa ni halartar tawagar zuwa Guyana."

Kasar Guyana dake arewa maso gabashin Latin Amurka, daya ce daga cikin kasashe mafiya fama da kangin talauci. Yadda ake samun matsala a fannin tattalin arziki, ya sa babu isassun likitoci a kasar. An ce akwai asibitoci 27 kacal a kasar, gami da likitoci fiye da 750.

Asibitin Georgetown asibiti ne mafi kyau cikin asibitocin kasar na jama'a, amma yana fuskantar matsalolin rashin kayayyaki masu inganci, da kwararrun ma'aikata, lamarin da ya sanya ya dogaro kan tallafi daga kasashen waje.

Tun bayan da kasar Sin ta fara tura likitocinta zuwa Guyana a shekarar 1993, likitoci Sinawa suna taka muhimmiyar rawa wajen aikin kula da marasa lafiya a asibitin Georgetown, inda suke tallafawa gudanar ayyukan asibiti na yau da kullum. Zhang Yueming ya tuna da cewa, bayan da shi da abokan aikinsa suka isa Georgetown a shekarar 2012, nan take sun fara aiki.

Zhang ya ce, "jami'an asibitin da na ma'aikatar lafiyar kasar suna fatan za mu iya fara aiki ba tare da wani bata lokaci ba. Hakan kuwa ya kasance wani kalubale ne gare mu, domin ba mu saba da muhallin kasar ba tukuna, amma mun fara aiki ba tare da wani jinkiri ba."

Bayan da Zhang da abokan aikinsa suka fara sabawa da muhallin kasar Guyana, an kara ba su wasu ayyuka masu wuya. Ta la'akari da manufar raba majiyyata da kasar Guyana ta dauka, inda ake kai majiyyatan da suka kamu da cututtuka masu tsanani zuwa manyan asibitoci masu kyau, hakan ya sa aka fi samun majiyyata masu fama da tsananin cututtuka a asibitin da Zhang Yueming yake aiki. Sa'an nan, sashin kula da mata da haihuwa ya kasance wani sashin da aka fi shan aiki. A matsayinsa na kwararren likita, Zhang Yueming ya yi kokarin lura da majiyyata da yawa, yayin da a dayan bangaren kuma, ya kan samar da taimako ga sauran likitocin da ke da bukata. Yadda yake shan aiki sosai ya kan hana shi samun damar cin abincin tsakar rana.

Zhang Yueming ya ce, "wasu majiyyata sun zo daga wurare masu nisa ta jirgin sama, ko kuma sun tashi karfe 4 na safe don su shiga jirgin ruwa, sa'an nan su sauya zuwa mota don zuwa wurinmu. Wadannan majiyyata, idan an kasa kula da su cikin lokaci, ba za su samu damar koma gida ba, ganin in ba haka ba za su sake jira har tsawon watanni 3 kafin su samu damar ganin likita. Duba da matsalar da suke fuskanta, ya sa na kan dakatar da cin abinci don kokarin jinyar mafi yawan su."

Guyana kasa ce da ke wuri mai zafi, don haka a kan samu wasu cututtuka masu sarkakiya da ba a taba ganinsu a kasar Sin ba. Amma Zhang Yueming da abokan aikinsa sun yi aiki tare, inda suka gudanar da ayyukan tiyata masu wuya daban daban, tare da kafa tarihi a fannin aikin jinyar kasar Guyana.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China