logo

HAUSA

‘Yan Sama Jannatin Da Ke Cikin Kumbon Shenzhou-13 Sun Shiga Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-3

2021-10-17 16:40:05 CRI

‘Yan Sama Jannatin Da Ke Cikin Kumbon Shenzhou-13 Sun Shiga Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-3_fororder_jirgi

Hukumar kula da ayyukan sararin samaniyar kasar Sin CMSA, ta sanar a yau Lahadi cewa, ‘yan sama jannati uku da ke cikin kumbon Shenzhou-13 sun shiga kumbon dakon kaya na Tianzhou-3 don shirya yin jigilar kayayyaki.

Bayan da‘yan sama jannatin uku da ke cikin kumbon na Shenzhou-13 wato su Zhai Zhigang, Wang Yaping, da Ye Guangfu suka shiga cikin babban akwatin Tianhe daya bayan daya, sun yi nasarar bude kofar kumbon dakon kaya na Tianzhou-3, kana sun shiga ciki da misalin karfe 9:50 na safe agogon Beijing, kamar yadda hukumar ta CMSA ta bayyana.

'Yan sama jannatin za su kuma bude kofar kumbon dakon kaya na Tianzhou-2. Za su yi jigilar kayayyaki da kuma gudanar da sauran ayyuka kamar yadda aka tsara.

An harba kumbon Shenzhou-13 mai dauke da ‘yan sama jannati 3 na kasar Sin ne daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan dake hamadar Gobi a arewa maso yammacin kasar Sin jiya Asabar 16 ga wata.

Bayan da kumbon Shenzhou-13 ya shiga hanyar da aka tsara a sararin samaniya, ya kuma yi nasarar hadewa da babban akwatin Tianhe. ‘Yan sama jannatin na kasar Sin wato su Zhai Zhigang, Wang Yaping, da Ye Guangfu sun shiga cikin babban akwatin Tianhe daya bayan daya. Za su kuma shafe tsawon watanni shida yayin tafiya a sararin samaniyar, ta haka za su kafa sabon tarihi a kasar Sin a fannin tsawon wa’adin ayyukan bincike a sararin samaniya.(Ahmad)

Ahmad