logo

HAUSA

Sin ta gabatar da sunayen ‘yan sama jannati da za su bi kumbon Shenzhou-13 a aikin binciken tashar sararin samaniya

2021-10-14 20:10:14 CRI

Sin ta gabatar da sunayen ‘yan sama jannati da za su bi kumbon Shenzhou-13 a aikin binciken tashar sararin samaniya_fororder_6d81800a19d8bc3edc6b457c04f9e217a9d345a4

A yau Alhamis ne hukumar lura da ayyukan ‘yan sama jannati ta kasar Sin ko CMSA a takaice, ta bayyana Zhai Zhigang, da Wang Yaping da Ye Guangfu, a matsayin ‘yan sama jannati 3 da za a harba samaniya cikin kumbon Shenzhou-13, inda za su yi aikin bincike a tashar samaniya ta Sin har tsawon watanni 6.

An bayyana Zhai Zhigang, a matsayin wanda zai jagoranci tawagar, kasancewar sa daya daga ‘yan sama jannati da suka bi kumbon Shenzhou-7 a shekarar 2008, wanda kuma ya yi aikin tafiya a sararin samaniya, aikin da ya kasance irin sa na farko da ‘yan sama jannati na kasar Sin suka gudanar.

Ita ma Wang Yaping, ta halarci aikin da aka gudanar da kumbon Shenzhou-10 a shekarar 2013, ita ce kuma Basiniya ta farko ‘yar sama jannati, da za ta ziyarci tashar sararin samaniya ta Sin, tare da gudanar da aiki a wajen na’urorin sufuri dake wurin.

A daya bangaren kuma, Ye zai bi kumbon Shenzhou-13, a tafiyarsa ta farko zuwa sararin samaniya, kamar dai yadda mataimakin daraktan hukumar CMSA Lin Xiqiang ya bayyana.

Lin ya ce ‘yan sama jannatin su 3, za su kasance a tashar binciken samaniya ta Sin har tsawon watanni 6, wa’adin da za a ci gaba da aiki da shi a nan gaba, yayin ayyukan ‘yan sama jannatin kasar Sin.  (Saminu)