logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi cikakkiyar nasarar harba kumbon Shenzhou 13

2021-10-16 09:45:28 CRI

Kasar Sin ta yi cikakkiyar nasarar harba kumbon Shenzhou 13_fororder_1e30e924b899a901dad9b1857fb34c720308f541

A sanarwar ofishin kula da ayyukan sararin samaniyar kasar Sin, da misalin karfe 12 da mintoci 23 na tsadar daren Asabar wato ranar 16 ga wata bisa agogon Beijing, an harba rokar LongMarch-2F da ke dauke da kumbon Shenzhou-13 bisa lokacin da aka tsara a cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan. Bayan kimanin dakika 582 kuma, kumbon Shenzhou-13 din ya yi nasarar rabuwa da rokar, sannan ya shiga inda aka kayyade. An yi nasarar tura ‘yan sama jannati uku, da suka hada da Zhai Zhigang, Wang Yaping, da Ye Guangfu zuwa sararin samaniya, yanzu dai suna cikin koshin lafiya.

Wannan aiki shi ne karo na 21 tun bayan tabbatar da gudanar da ayyukan sararin samaniya masu dauke da ‘yan saman jannati na kasar Sin, kana aiki na biyu mai dauke da ‘yan sama jannati ne a matakin tashar sararin samaniya na ayyukan.(Bilkisu)