logo

HAUSA

Sin na shirin harba kumbon Shenzhou-13 don binciken sararin samaniya

2021-10-07 15:13:52 CRI

Sin na shirin harba kumbon Shenzhou-13 don binciken sararin samaniya_fororder_shenzhou

Hukumar kula da ayyukan kumbon dauke da mutane ta kasar Sin CMSA, ta sanar a yau Alhamis cewa, ta riga ta tura kumbon dauke da mutane na Shenzhou-13 da rokar Long March-2F zuwa cibiyar harba tauraron dan Adam ta kasar, kuma nan da wani lokaci ana sa ran za ta harba kumbon domin gudanar da ayyukan bincike.

CMSA ta ce, kayayyaki da na’urorin da aka kai cibiyar harba tauraron dan Adam din suna cikin yanayi mai kyau, kuma tuni aka gudanar da wasu gwaje gwaje masu yawa don tantance ingancinsu, kana za a gudanar da wani aikin gwajin na’urorin na hadin gwiwa a nan gaba kamar yadda aka tsara.(Ahmad)