logo

HAUSA

BRICS Sun Tsara Taswirar Hanyar Zuba Jari Da Cinikayya

2021-09-07 11:08:39 CRI

BRICS Sun Tsara Taswirar Hanyar Zuba Jari Da Cinikayya_fororder_jin

An gudanar da taron ministocin tattalin arziki da cinikayya na kasashen BRICS karo na 11 ta kafar bidiyo a ranar 3 ga wata.

Chen Chao, mataimakin babban direktan sashen harkokin waje na ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana jiya a nan Beijing cewa, a yayin taron, ministocin sun yi alkawarin zurfafa hadin gwiwar duniya wajen yaki da annobar COVID-19, sun amince da kiyaye tsarin yin ciniki tsakanin sassa daban daban da tsai da kudurin kyautata hadin gwiwar a-zo-a-gani ta fuskar tattalin arziki da ciniki. Chen ya yi karin bayani cewa, an zartas da wasu takardun hadin gwiwa a fannonin cinikayyar hidimomi, da ikon mallakar fasaha, da yin kasuwanci ta yanar gizo da dai sauransu, tare da tsara taswirar hanyar zuba jari da cinikayya karkashin manyan tsare-tsaren BRICS dangane da tattalin arziki nan da shekarar 2025.

Yawan mutanen da suke zaune a kasashen BRICS wato Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta kudu ya wuce kaso 40 cikin dari bisa jimilar mutanen duniya, yayin da yawan dukiyoyin zaman al’ummar kasashen ya kai kaso 24 cikin dari bisa na duniya. Chen Chao ya nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da fadada fannonin yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashen BRICS ta fuskar tattalin arziki da ciniki, a kokarin kara kaimi kan farfadowar tattalin arzikin duniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan