logo

HAUSA

Hadaddiyar sanarwar BRICS game da cudanyar bangarori daban daban ta dace da ra’ayoyin da kasa da kasa

2021-06-07 21:12:03 CRI

Ministocin harkokin wajen kasashen BRICS sun zanta ta wayar tarho ta kafar bidiyo a ranar 1 ga wannan wata, inda suka bayar da hadaddiyar sanarwar BRICS, game da sa kaimi ga ingantawa, da aiwatar da kwaskwarima ga tsarin cudanyar bangarori daban daban.

Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, sanarwar ta shaida fatan bai daya na yawancin kasashen duniya, wadda ta dace da ra’ayoyin da kasa da kasa suka amincewa.

Wang Wenbin ya ce, kasashen BRICS sun jaddada cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka kan ka’idoji da kundin tsarin MDD, da kin amincewa da ra’ayoyin yin watsi da kasashen waje, da daukar ma’auni 2 kan batutuwa, da kin manufar kama karya, da ra’ayin yin takara a tsakanin kasa da kasa, wadda ke fatan haifar da riba cikin hasarar da sauran kasashe suka tabka, da kauracewa yin takara a fannin siyasa da tsarin kasa, da kuma kaucewa tsai da kuduri ba tare da yin bincike ba.

Ya ce Sin ta yi imanin cewa, sanarwar ta dace da hakikanin abubuwa, ta kuma dace da yanayin da ake ciki, kuma babu shakka za ta samu amincewa, da goyon baya daga karin kasashen duniya. (Zainab)